Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Ta Ce Ba Zata Janye Sojojinta Daga Bakin Iyakar Pakistan Ba Sai Bayan Oktoba - 2002-06-28


Indiya ta ce ab zata iya janye sojojinta daga bakin iyaka da Pakistan a yanzu ba, har sai bayan zaben da za a yi cikin watan Oktoba a bangaren Indiya na Kashmir, inda aka kashe mutane 19 a hare-hare jiya alhamis.

Ministan tsaron Indiya, George Fernandes, shi ya bayyana wannan a yayin da ake nuna fargaba a birnin New Delhi kan cewa 'yan tsagera dake da cibiya a Pakistan zasu yi kokarin wargaza zaben da za a yi.

Ya ce a bayan zaben, janye sojojin zai dogara kan halin da ake ciki a yankin.

'Yan sandan Indiya suka ce a hare-haren jiya alhamis da ake tsammanin Musulmi 'yan aware ne suka kai, an kuma raunata wasu mutane 26.

An ci gaba da tashe-tashen hankula a Kashmir, duk da sassautowar zaman tankiya cikin watan nan a tsakanin Indiya da Pakistan. Kasashen biyu masu gaba da juna, sun girka sojoji fiye da miliyan daya a bakin iyakarsu.

XS
SM
MD
LG