Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sa'udiyya Ta Caccaki Shirin Shugaba Bush Game Da Gabas Ta Tsakiya - 2002-06-30


Babbar kawar Amurka a yankin Gulf, Sa'udiyya, ta yi tur da shirin da shugaba Bush ya gabatar na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Cikin hirar da yayi da wata jaridar Larabci da ake bugawa a London, Yarima Nawaf bin Abdul-Aziz, ya ce kiran da Mr. Bush yayi na a kawar da Malam Yasser Arafat daga kan mulki, yana iya dagula kokarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Yarima Nawaf, shugaban hukumar leken asirin Sa'udiyya, kuma dan'uwan Sarki Fahd, ya ce shawarwarin da Mr. Bush ya bayyana a ranar litinin, koma baya ce sosai daga amincewar da yayi da shirin samar da zaman lafiyar da Sa'udiyya ta gabatar.

Sa'udiyya tayi marhabin da wasu bangarorin shirin na Mr. Bush, amma ta bayyana takaicin cewa shugaban bai soki manufofin Isra'ila ba.

A can birnin Amman, sarki Abdullahi na Jordan yayi marhabin da kiran da shugaba Bush yayi na kafa kasar Falasdinu, amma kuma ya ce tilas ne kafa wannan kasa ya zamo cikakke kuma ta yin la'akari da bakin iyakokin yankin kafin shekarar 1967. Ya ce tilas a kafa wannan kasa ba tare da jinkiri ba idan har ana son yin haka ya taimaka wajen kwantar da wutar tarzoma.

XS
SM
MD
LG