Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Yin Tur Da Hukumomin Kasar Liberiya... - 2002-07-04


Wata sananniyar kungiyar kare hakkin Bil Adama ta nuna rashin jin dadin yadda hukumomin Liberiya suka tsare editan wata jarida mai zaman kanta tare da wasu mutanen uku bisa zargin cewa suna kulla makrkashiyar kashe shugaban kasar.

A cikin sanarwar da ta bayar a yau alhamis, kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" mai hedkwata a birnin New York, ta zargi hukumomin Liberiya da laifin kamawa da kuma cin zarafin editan jaridar "Analyst" ta Afirka ta Kudu, Hassan Bility.

Tun ranar 24 ga watan yuni aka kama Mr. Bility tare da wasu 'yan Liberiya su uku. An tuhume shi da laifin taimakawa 'yan tawayen da ake zargin wai suna kulla makarkashiyar kashe shugaba Charles Taylor.

A jiya laraba, kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Amnesty International" mai hedkwata a London, ta ce watakila an ganawa Hassan Bility da sauran fursunonin azaba aka kashe su a cikin kurkuku.

Jami'an gwamnati sun tabbatarwa da jama'a cewa har yanzu fursunonin suna nan da ransu.

XS
SM
MD
LG