Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bukukuwan Ranar Samun 'Yanci A Amurka - 2002-07-04


Shugaba Bush ya yi kira ga Amurkawa da su saki jikinsu, su more hutun da ake yi yau alhamis, hudu ga watan Yuli, domin tunawa da ranar da Amurka ta samu 'yancin kanta.

Wannan shine hutun ranar 'yanci na farko da za a yi tun bayan harin ta'addanci na 11 ga watan Satumbar bara.

A halin da ake ciki dai, 'yan sanda, da jami'an hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, FBI, da kuma sojoji, sun tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar. Jiragen yakin sojojin Amurka kuma suna yin sintiri a sararin samaniyar nan Washington, babban birnin kasar.

Dukkan wani dan sanda dake nan Washington, yana aiki yau alhamis, inda can da an jima kuma, jami'an tsaro na hukumar FBI cikin kayan farar hula, za su saje da dimbin jama'ar da ake kyautata zaton, zasu hallara domin wasan wutar da aka saba yi bisa al'ada, a irin wannan rana ta mulkin kai.

Su ma dai, sauran biranen Amurka, suna daukar irin wadannan matakan tsaro, yayin da su kuma dogarawan tsaron cikin gida na musanman, (National Guard) suke gadin muhimman gadoji da titunan karkashin kasa.

Koda yake hukumar FBI ta gabatarwa da 'yan sanda wata sanarwa kan bukatar zama cikin shirin ko-ta-kwana, saboda yiwuwar kawo farmakin ta'addanci, amma kuma hukumar ba ta yi wani tartibin bayani ba, gameda wuraren da maiyuwa za a iya kai wa farmakin.

XS
SM
MD
LG