Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zaben Kananan Hukumomi Da Birane A Kasar Ivory Coast - 2002-07-08


A kasar Ivory Coast, dubban 'yan takara sun fafata a zaben da aka yi jiya lahadi, domin samun kujerar wakilci daga cikin kujeru fiye da dubu biyu da ake da su a gundumomin kasar hamsin da takwas.

An kasance cikin zaman dar-dar, a sakamakon gardama da ta kaure gameda katin shaidar kada kuri'a wanda hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bukata a lokacin zaben na jiya.

Madugun 'yan adawa, Malam Alassane Ouattara, ya yi korafin cewa yawancin magoya bayansa, ba su samu sabon katin rajistar ba.

Wakilin Muryar Amurka a Abidjan, babban birnin Ivory Coast din, ya ce mutane ba su fito ba sosai, inda a yawancin gundumomi dake birnin, aka bada rahoton cewa, da kadan mutanen da suka jefa kuri'sunsu suka haura kashi goma cikin dari.

Ana daukar wannan zabe, tamkar wani gwaji gameda yadda al'amura a kasar ta Ivory Coast suke komawa kamar yadda aka saba, kafin juyin mulkin da sojoji suka yi, a shekarar dubu da dari tara da 99 wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 300.

Ana kuma kallon zaben na jiya a matsayin wani mizani na auna tagomashi, ko kuma goyon bayan da gwamnatin Shugaba Laurent Gbagbo take da shi.

XS
SM
MD
LG