Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Na Iraqi Suna Tattauna Yadda Zasu Hambarar Da Saddam Hussein - 2002-07-13


Tsoffin jami'an sojan Iraqi da 'yan adawar kasar sun fara tattaunawa a London, kan hanyoyin da zasu iya bi domin hambarar da shugaba Saddam Hussein.

Jami'an suka ce wannan taro da aka fara jiya Jumma'a ya maida hankali ne kan kafa gwamnatin dimokuradiyya a Iraqi, tare da sanya rundunar sojojin Iraqi a karkashin ikon fararen hula a bayan an tumbuke Saddam Hussein daga mulki.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, ya ce tattaunawar ta London lamari ne mai muhimmanci, kuma jami'an diflomasiyya daga ofishin jakadancin Amurka a London zasu halarci taron.

Shugaba Bush ya ce Amurka zata yi amfani "da dukkan matakan da zata iya" dauka domin tumbuke Saddam Hussein, wanda take zargi da goyon bayan ta'addanci tare da kokarin mallakar makaman kare dangi.

Kasashen Kuwaiti da Jordan makwabtan Iraqi dai, sun fito fili sun musanta rahotannin cewar Amurka zata yi amfani da yankunansu domin kai hari kan Iraqi.

XS
SM
MD
LG