Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da MDD Sun Sasanta Rikicin Kafa Kotun Shari'ar Laifuffukan Yaki Ta Duniya - 2002-07-13


Ba tare da wata hamayya ba, Kwamitin Sulhun MDD ya zartas da kudurin da ya bai wa sojojin Amurka masu aikin kiyaye zaman lafiya kariyar wucin gadi daga bayyana gaban sabuwar kotun shari'ar manyan laifuffuka ta duniya bisa tuhumar aikata laifuffukan yaki.

Wannan kudurin da aka zartas cikin daren Jumma'a, na sasantawa ne da aka cimma a tsakanin Amurka da Faransa da kuma Britaniya.

Kudurin ya bada kariyar shekara guda ta binciken aikata laifuffukan yaki a kan sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashen da basu rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kafa wannan kotu ba. Wadannan kasashe sun hada da Amurka, da Iraqi, ad China da kuma Afghanistan.

Amurka dai ta so ne a ba ta kariya ta har abada cewar ba za a gurfanar da sojojinta gaban wannan kotu ba, a saboda tana fargabar cewa za a iya yin amfani da muradun siyasa wajen tuhumar sojojinta gaban wannan kotu.

XS
SM
MD
LG