Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Louis Farrakhan Ya Ce Al'ummar Iraqi Ne Suke Da Ikon Canja Gwamnatinsu Ba Wani Ba - 2002-07-15


Shugaban kungiyar Musulmi ta "Nation of Islam" ta Amurka, Louis Farrakhan, ya ce Amurka ba ta da ikon neman canja gwamnati a kasar Iraqi.

Shugaban Musulmin bakar fata na Amurka ya ce al'ummar Iraqi ne suke da ikon cire shugaba Saddam Hussein daga kan mulki idan ba su kaunarsa.

A lokacin da yake magana cikin shirin "Late Edition" na gidan telebijin din CNN, Malam Farrakhan ya ce Amurka ba ta da ikon yin katsalanda a harkokin cikin gida na wata kasa.

Malam Farrakhan ya ziyarci birnin Bagadaza a makon da ya shige, ya kuma gana da jami'an Iraqi da dama, amma kuma bai gana da shugaba Saddam ba. Ya ce ya kai wannan ziyara ce a wani bangaren kokarin tallafawa shirin samar da zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, da kuma hana kai hare-haren soja a kan Iraqi.

XS
SM
MD
LG