Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Biyar Suka Hallaka A Tel Aviv - 2002-07-18


Mutane akalla biyar sun mutu a wasu hare-haren da ake kyautata zaton tagwaye ne na kunar-bakin-wake a birnin Tel Aviv. 'Yan sanda sun yi imanin cewa biyu daga cikin wadanda suka mutu wadanda suka kai harin ne. An bada rahoton cewa wasu mutanen su 30 kuma sun ji rauni.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Qudus, ya ce 'yan sandan Isra'ila suna zaton cewa wannan lamari da ya faru a kusa da tsohuwar tashar motocin safa a kudancin Tel Aviv, makarkashiya ce kullalliya da ta shafi tagwayen masu kai harin kunar bakin wake.

An killace wannan yanki a yayin da motocin jigilar marasa lafiya da 'yan sanda suka isa wurin domin kwashe wadanda suka ji rauni, tare da binciken ko akwai wasu nakiyoyin.

Gidan rediyon Isra'ila ya ce da yawa daga cikin wadanda suka mutu ma'aikata ne 'yan kasashen waje. Wannan hari ya faru a gundumar dake makare da kananan kantuna da teburorin masu talla, kuma akasarin mazaunanta baki ne 'yan kasashen waje.

Minista a majalisar mulkin kan Falasdinawa, Saeeb Erekat, yayi tur da harin, yana mai fadin cewa yana adawa da duk wani matakin kashe fararen hula, ya Allah Falasdinawa ne ko kuma yahudawa. Ya ce hanya guda ta kawo karshen wannan tashin hankali ita ce Isra'ila ta kawo karshen mamayar sojan da tayi wa Yammacin kogin Jordan da zirin Gaza.

Gwamnatin Isra'ila, kamar yadda ta saba yi, ta dora laifin harin a kan shugaban Falasdinawa Yasser Arafat. Kakakin gwamnatin Isra'ila, Avni Pazner, ya ce Malam Arafat bai yi wani kokarin kawo karshen zubar da jini da kashe kashen da watakila za a ci gaba da su muddin yana kan karagar mulki ba. A cewarsa, Isra'ila ba ta da wani zabi illa ta ci gaba da mamaye yankin yammacin kogin Jordan da sojoji masu yawa har sai an kawo karshen hare-haren, su kuma Falasdinawa suka zabi sabon shugaba wanda ke son yin zaman lafiya da kasar Bani yahudu.

XS
SM
MD
LG