Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsuke Hanyoyin Bada Biza Ga 'Yan Saudi Arabiya - 2002-07-21


Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta soke wani tsari mai farin jini, amma wanda ake yin takaddama a kai, na bada takardun iznin shigowa Amurka ga 'yan Sa'udiyya ta hannun kamfanonin tafiye-tafiye.

Daga jiya asabar, ofishin jakadancin Amurka dake birnin Riyadh ya daina karbar takardun neman biza ta hannun wani dabam idan ba mutumin dake son yin tafiya da kansa ba.

Wata mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen, ta ce an soke wannan shirin a saboda rahotannin da kafofin labarai suka yi ta bayarwa, dake nuna kamar haka kawai jami'ai suke bada takardun biza ba tare da sun binciki mai niyyar tahowa Amurka ba.

'Yan majalisar dokokin Amurka da dama sun soki wannan shirin bada takardun bizar ga 'yan Sa'udiyya ta hannun wani kamfani dabam. Suka ce da yawa daga cikin wadanda suka yi fashin jiragen sama na ranar 11 ga watan Satumba sun samu takardun iznin shigowa Amurka ta yin amfani da wannan shiri ne.

XS
SM
MD
LG