Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce A Shirye Yake Ya Rattaba Hannu A Kan Dokar Hukumta Mazambatan Shugabannin Kamfanoni - 2002-07-26


Shugaba Bush ya ce a shirye yake ya rattaba hannu a kan dokar hukumta yin zama a kamfanoni, wadda majalisar dokokin tarayya ta zartas jiya alhamis da gagarumin rinjaye.

Wannan kudurin dokar da majalisun wakilai da dattijai suka zartas ta kara tsananin hukumcin da za a yi wa shugabannin manyan kamfanoni da aka samu da laifin yin zamba, tare da bai wa masu zuba jarin da aka zambata karin lokacin shigar da kara a kotu.

Shugaba Bush ya ce sabuwar dokar zata taimakawa masu zuba jari da ma'aikatan manyan kamfanoni a fadin Amurka, ta hanyar ba su karin kwarin guiwar cewa shugabannin irin wadannan kamfanoni suna fadin gaskiya cikin bayanai da rahotanninsu.

Shugaban na Amurka tare da shugabanni a majalisar dokoki, sun bukaci da a gaggauta zartas da wannan doka domin takalar rahotannin abubuwan fallasar da suka yi ta fitowa kan yadda shugabannin manyan kamfanoni ke facaka da kudi, ko boye sawun kudin. Wadannan rahotanni sun taimaka wajen tankwasa keyar darajar hannayen jari zuwa kasa warwas a kasuwannin hada-hadarsu a nan Amurka.

XS
SM
MD
LG