Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Harkokin Waje Tace Tana Daukar Barazana Da Gaske - 2002-07-27


Ma'aikatar harkokin waje tana dauka da gaske sosai, barazanar da aka yi cewar nan da mako guda, 'yan ta'adda zasu ragargaza dukkan ofisoshin jakadancin Amurka dake kasashen Musulmi.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen ya shaidawa Muryar Amurka cewa sai yanzu suke jin labarin wannan barazana ta cikin wayar tarhon da aka bugawa kafofin yada labarai na Amurka a ranar alhamis da maraice.

Mutumin da ya buga wayar, ya ce shi kakaki ne na shugaban kungiyar 'yan ta'adda ta al-Qa'ida, Osama bin Laden.

Jami'in ma'aikatar harkokin wajen ya ce hukumomin Amurka ba zasu iya gaskata ko wanene a zahiri ya buga wannan wayar ba.

Jami'in ya ce tuni da ma dai an dauki matakan tsaro masu yawa a dukkan ofisoshin jakadancin Amurka dake kasashen waje. Bai bayyana ko wasu irin matakai za a kuma sake dauka yanzu ba, idan har za a yi hakan.

XS
SM
MD
LG