Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan Tana Karbar Bakuncin Taron Duniya Kan Nakiyoyi - 2002-07-28


Yau lahadi a birnin Kabul shugaba Hamid Karzai na Afghanistan zai bude taron kasashen duniya a kan haramta dasa nakiyoyi.

Wakilai suna fatan cewa Mr. Karzai zai cika alkawarin da ya dauka na rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haramta Dasa Nakiyoyi Ta Duniya a lokacin wannan taron kwanaki uku. Yarjejeniyar ta 1997 ta haramta dasawa, ko kerawa ko tara nakiyoyin da akan binne a kasa.

Kwararru suka ce Afghanistan tana daya daga cikin kasashen da aka fi dasa nakiya cikinsu a duk fadin duniya.

MDD ta ce mutane har 300 suke mutuwa ko suke jin rauni a kowane wata a sanadin nakiyoyi da albarusan dake warwatse a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG