A kwanakin baya ma'aikatan sashen Hausa suka taru domin daukar hotunan da za a yi amfani da su cikin sabuwar kalanda a shekara ta 2003.
Ma'aikatan da suke aikin dare da wadanda ke aikin rana duk sun hallara, domin tabbatar da cewa a bana, ba kamar shekarar da ta shige ba, wannan sashe ba zai zauna a baya ba.
Sabuwar kalandar shekarar 2003, zata fito a wajejen watan Oktoba ko Nuwambar wannan shekarar ta 2002.