Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Kurdawa Ya Ce Ba Su Yanke Shawarar Ko Zasu Goyi Bayan Shirin Amurka Na Kai Hari Kan Iraqi Ba - 2002-08-07


Madugun daya daga cikin kungiyoyin Kurdawa biyu dake rike da yankin arewacin Iraqi ya ce har yanzu ba su yanke shawarar ko zasu goyi baya, ko kuma shiga cikin shierye-shiryen Amurka na hambarar da shugaba Saddam Hussein daga kan mulki.

Jalal Talabani na kungiyar Kurdawa ta PUK, yayi magana yau laraba a babban birnin kasar Turkiyya, a bayan da ya gana da jami'ai a ma'aikatar harkokin waje.

Mr. Talabani, wanda zai iso nan birnin Washington gobe alhamis, ya shaidawa 'yan jarida cewa yana son tabbaci daga gwamnatin shugaba Bush cewar duk wani matakin hambarar da Saddam Hussein zai kai ga tabbatar da hadaddiyar kasar Iraqi mai bin tafarkin dimokuradiyya.

Ya ce idan aka samu irinwannan tabbaci, yayi imanin za a iya kafa kawancen adawa mai karfin gaske domin kalubalantar mahukumta a birnin Bagadaza.

XS
SM
MD
LG