Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Condoleeza Rice Da Colin Powell Zasu Gana Da Ministocin Falasdinawa - 2002-08-08


Wata tawagar ministocin Falasdinawa zata gana da mai bai wa shugaba Bush shawara kan harkokin tsaron kasa, Condoleeza Rice, da sakataren harkokin waje, Colin Powell, yau alhamis a nan Washington.

Wannan ita ce ganawar farko ta manyan jami'an Amurka da Falasdinawa da za a yi tun cikin watan Yuni, a lokacin da shugaba Bush ya yi kira ga Falasdinawa da su zabi shugabannin da ta'addanci bai bata su ba. Amurka tana zargin shugaban Falasdinawa, yasser Arafat, da laifin kasa hana kai hare-haren ta'addanci a kan Isra'ila.

Tawagar ta Falasdinawa ta kunshi ministan harkokin cikin gida, Abdel-Razak Yahiya, da ministan tattalin arziki, Maher el-Masri, mutane biyun da Mr. Powell ya yabawa a watan da ya shige a zaman masu kokarin yin garambawul ga majalisar mulkin kan Falasdinawa.

Amma kuma shugaban tawagar, Saeb Erekat, ya shaidawa 'yan jarida a nan washington cewa shi har yanzu yana biyayya ga Malam Arafat. yayi kashedin cewa maye gurbin shugaban na Falasdinawa zai haddasa fitina.

XS
SM
MD
LG