Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda Ta Yarda Zata Janye Daga Kwango Kinshasa - 2002-08-15


Manyan jami'an Kwango da na Uganda sun rattaba hannu kan yarjejeniya da nufin kulla dangantaka a bayan yakin shekaru hudu.

A karkashin yarjejeniyar, Uganda tayi alkawarin janye sojojinta daga Kwango Kinshasa. Manyan ministocin kasashen biyu suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a bayan tattaunawar kwanaki uku a Luanda, babban birnin Angola.

Har yanzu ba fahimci ko yaushe ne Uganda zata fara janye sojojinta daga Kwangon ba.

makonni biyu da suka shige, gwamnatocin Rwanda da Kwango Kinshasa sun rattaba hannu kan irin wannan yarjejeniya ta zaman lafiya.

Kama daga shekarar 1998, Uganda da Rwanda sun goyi bayan 'yan tawayen dake neman hambarar da gwamnatin Laurent Kabila, mahaifin shugaban kasar na yanzu, Joseph Kabila.

Su kuma kasashen Angola da Zimbabwe da Namibiya sun tura sojojinsu domin goyon bayan gwamnatin Kwango Kinshasa.

XS
SM
MD
LG