Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Maida Makamashin Uranium Na Yugoslavia Zuwa Rasha - 2002-08-23


Jami'an Yugoslaviya da Rasha da na Amurka sun ce an yi jigilar makamashin Uranium tatacce da za a iya hada makami da shi, daga wata masana'antar nukiliya ta Yugoslaviya, zuwa wani wuri mai tsaro a kasar Rasha.

Wannan aikin jigila da aka yi shi cikin tsaro sosai, na hadin guiwa ne a tsakanin sojoji da 'yan sandan Yugoslaviya tare da ma'aikata daga ma'aikatar makamashi ta kasar Rasha, wadanda suka kwashe rododi guda dubu 6 na Uranium.

Jami'an Amurka sun taimaka wajen shiryawa da samar da kudin gudanar da aikin jigilar makamashin na Uranium, wanda aka ce yawansa ya kai na hada bam din nukiliya guda biyu.

A nan Washington, jami'an Amurka sun ce wannan aiki yana da muhimmanci a saboda Rasha ta yarda ta karbi makamashin na nukiliya wanda tun zamanin Tarayyar Soviet aka bai wa Yugoslaviya, domin ta sake tace shi.

XS
SM
MD
LG