Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilai A Zauren Taron Alkinta Muhalli Na Duniya Sun Soki Amurka Da Turai - 2002-08-27


Wakilai a zauren taron kolin duniya kan alkinta muhalli, sun yi kira ga Amurka da kasashen Turai da su rage yawan rangwamen da suke bai wa manomansu, ta yadda kasashe masu tasowa zasu iya yin takara da su a kasuwannin amfanin gona na duniya.

A yau talata aka koma ga tattaunawa a birnin Johannesburg a kasar Afirka ta Kudu, inda batun noma da ake cacar-baki sosai a kai ya mamaye ajandar taro.

A yayin da yankin kudancin Afirka yake fuskantar bala'in fari, wakilan kasashe masu tasowa sun yi kira ga kasashen duniya masu arziki da su dauki matakan zabtare irin rangwamen da suke yi wa farashin amfanin gonar kasashensu.

Sun zargi Amurkawa da Turawa da laifin kin yarda su tattauna tsarin cinikayya na duniya, suna masu fadin cewa rangwamen farashin yana hautsina kasuwannin amfanin gona na duniya domin amfanin su kasashen masu arziki.

Manufar wannan taron koli na kwanaki goma, ita ce rage yawan talauci a duniya tare da alkinta muhalli.

XS
SM
MD
LG