Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijeriya Yana Fuskantar Wata Sabuwar Barazanar - 2002-08-28


Majalisar dattijan Nijeriya ta jefa kuri'ar fadada binciken shugaba Olusegun Obasanjo.

Kuri'ar da majalisar ta jefa jiya talata, tayi kama da kudurin da majalisar wakilan kasar ta zartas makonni biyun da suka shige, inda ta zargi shugaban da laifin zarmiya da rashin iya gudanar da mulki. Wakilan majalisar sun bukace shi da yayi murabus a ranar litinin da ta shige ko kuma su tsige shi.

'Yan majalisar sun bukaci sanin dalilin da ya sa gwamnatin shugaba Obasanjo ta kasa aiwatar da kasafce-kasafcen kudin da aka zartas tun daga shekarar 1999.

A jiya talata, wakilan majalisar wakilai sun yi zama, amma kuma ba su yanke shawarar ko zasu ci gaba da kokarin neman tsige shugaban ba. Zasu sake nazarin wannan batu a ranar 4 ga watan Satumba.

Mr. Obasanjo yayi watsi da yunkurin tsige shin a zaman "almarar da ta shige gona da iri, ko kuma wasan yara."

Wasu masu goyon bayan Mr. Obasanjo sun yi ikirarin cewa barazanar tsige shugaban, wani yunkuri ne da abokan adawarsa suke yi na bata masa suna kafin zaben da za a yi a cikin shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG