Shugaba Mohammed Khatami na kasar Iran ya ja kunnen Amurka game da kai wa kasarsa harin soja, yana mai cewa yin haka zai haddasa rashin kwanciyar hankali a fadin yankin Gabas ta Tsakiya.
Malam Khatami ya ce Iran zata yi bakin kokarinta domin kawar da duk wani abinda za a iya yin amfani da shi a zaman hujjar neman cin zalin kasarsa a fagen soja. Amma kuma ya lashi takobin cewa Iran zata kare 'yancinta da kuma muradunta idan har aka kai mata hari.
A lokacin da yake ganawa da 'yan jarida yau laraba a birnin Teheran, shugaba Khatami yayi kiran da a samu abinda ya kira "manufofi managarta" daga Amurka. Ya ce irin akidar da gwamnatin shugaba Bush ta runguma a yanzu, ta tsageranci ce, kuma zata iya nakkasa muradun Amurka.
Har ila yau ya sake jaddada adawarsa da kai harin soja a kan Iraqi, yana mai kashedin cewa yin haka zai yamutsa al'amuran tsaron duniya baki daya.