Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamid Karzai Ya Koma Kabul, Kwana Guda A Bayan Da Ya Tsallake Rijiya Da Baya - 2002-09-06


Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya koma birnin Kabul a yau Jumma'a, kwana guda a bayan da ya kubuta daga wani yunkuri na neman kashe shi a birnin Kandahar dake kudancin kasar.

Hukumomin Afghanistan sun ce sun yi amanna mabiyan al-Qa'ida da Taleban ne suka kitsa wannan hari na jiya alhamis.

Rahotanni daga Afghanistan sun ce mutumin da ya kai harin, sabon dogari ne a Kandahar, wanda ya fito daga tungar 'yan Taleban dake lardin Helmand a kudancin kasar. Maharin yana sanye da rigar soja, kuma sojojin Amurka dake tsaron lafiyar shugaba Karzai sun bindige, suka kashe shi.

An kashe wasu mutanen biyu. Haka kuma gwamnan Kandahar, Gul Agha Sherzai, da wani sojan Amurka sun ji rauni.

Sa'o'i kadan kafin wannan harin da aka kai wa Mr. Karzai, wani bam mai karfin gaske ya fashe a wata gunduma ta kasuwanci a birnin Kabul. An samu rahotannin da suka sabawa juna kan yawan mutanen da suka mutu. 'Yan sanda sun ce an kashe mutane 10, amma kafofin yada labarai an Afghanistan sun ce mutane har 30 suka mutu.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

Wadannan hare-hare sun kara yawan kiraye-kiraye daga kasashen duniya na kara matakan tsaro a Afghanistan. A halin yanzu dai, rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa tana aiki ne kawai a birnin Kabul.

XS
SM
MD
LG