Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai  Zata Baiwa Madagascar Dala Miliyan 572 Cikin Shekaru Biyar - 2002-09-06


Kungiyar Tarayyar Turai, KTT, zata bai wa kasar Madagascar agajin kudi dala miliyan 572 cikin shekaru biyar masu zuwa, abinda ya kawo karshen takunkumin bada agajin kudin da tarayyar ta sanyawa Madagascar a farkon shekarar nan.

Shugaban majalisar zartaswar tarayyar Turai, Romani Prodi, shi ya bada sanarwar wannan agaji a lokacin ad ya ziyarci wannan tsibiri dake cikin tekun Indiya.

Jami'in an KTT ya ce ya samu kwakkwaran alkawari daga shugaba Marc Ravalomanana kan cewa zai shimfida mulkin dimokuradiyya a kasar.

Mr. Ravalomanana da abokin adawarsa, tsohon shugaba Didier Ratsiraka, sun yi watani 7 suna gardama a kan ko wanene shugaban kasar na halal, a bayan zaben da aka yi cikin watan Disamba. daga baya, kotun kolin Madagascar ta ayyana Mr. Ravalomanana a zaman wanda ya lashe zaben.

XS
SM
MD
LG