Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mandela Yayi Tur Da Martanin Da Amurka Ta Maida Game Da Tayin Iraqi - 2002-09-17


Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, yayi tur da Amurka a saboda martanin ko ohon da ta mayar dangane da sanarwar Iraqi cewar zata kyale sufetocin makamai na MDD su koma cikin kasarta.

A lokacin da yake magana yau talata da 'yan jarida a gidansa a birnin Johannesburg, Mr. mandela ya kalubalanci ikon da shugaba Bush na Amurka yake da shi na yin tababar sahihancin tayin Iraqi, yana mai zargin Amurka da kokarin nunawa duniya fin karfi.

Mr. Mandela yayi kira ga sauran shugabannin duniya da ba su yarda da wannan lamari ba, da su fito a fili su bayyana adawarsu ga matsayin na Amurka.

Amurka dai tayi fatali da tayin Iraqi, tana mai cewa dabara ce kawai ta kaucewa harin soja daga Amurka. Jami'an Amurka sun yi kiran da a zartas da sabon kuduri mai tsaurin gaske kan Iraqi a Kwamitin Sulhun MDD.

XS
SM
MD
LG