Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Tana Shirye-Shiryen Tura Sufetocin Makamai Zuwa Iraqi, Yayin Da Shugaba Bush Yake Bayyana Cewa Dabara Kawai 'Yan Iraqi Suke Yi - 2002-09-18


Da alamun MDD tana ci gaba da shirye-shiryen mayar da sufetocin makamanta zuwa Iraqi, yayin da shugaba Bush na nan Amurka yake yin watsi da tayin Iraqi na kyale sufetocin su koma ba tare da tsangwama ba a zaman wata dabara ta yaudara.

Nan gaba a yau babban sakataren MDD, Kofi Annan, zai gana da ministan harkokin wajen Irqaqi, Naji Sabri.

Shi kuma babban sufeton makamai na MDD, Hans Blix, zai yi tattaki zuwa New York domin ya gana da Kwamitin Sulhun MDD a gobe alhamis.

A yau laraba kuma, Mr. Bush ya sake yin kira ga MDD da ta zartas da wani sabon kuduri mai tsauri a kan Iraqi. Har ila yau shugaban ya ce nan da 'yan kwanaki kadan zai gabatarwa da majalisar dokokin Amurka daftarin wani kudurin da zai ba shi iznin daukar matakan soja a kan Iraqi.

XS
SM
MD
LG