Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Ruwan Fito Na Fasinja Ya Nutse A Kasar Senegal Dauke Da Mutane 800 - 2002-09-27


Jami'ai a kasar senegal sun ce mutane kimanin 700 sun bace a bayan da wani jirgin ruwan fito na fasinja ya nutse a dab da gabar kasar Gambiya.

Firayim ministar kasar Senegal, Madame Madior Boye, ta ce an tabbatar da mutuwar mutane 41, a bayan da iska mai karfin gaske ta kifar da wannan jirgin ruwa mallakar gwamnati mai suna Joola da maraicen alhamis. Gwamnati ta ce ya zuwa yanzu, an ceto mutane 60.

Wannan jirgin ruwa ya taso ne daga lardin Casamance na kudancin Senegal zuwa Dakar, babban birnin kasar. Yana dauke da mutane kusan 800.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce an kera wannan jirgi ne domin ya dauki mutane 550.

Gwamnati ta ayyana zaman makokin kwanaki uku, daga yau Jumma'a.

XS
SM
MD
LG