Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Da MDD Suna Tattauna Komawar Sufetocin Makamai - 2002-09-30


Jami'an MDD sun ce an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi yau litinin da hukumomin Iraqi a kan batun komawar sufetocin makamai na majalisar zuwa Iraqi.

Sai dai kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta ce har yanzu da sauran aiki a gaba kafin sufetoin MDD su fara farautar makaman kare-dangi a fadin kasar Iraqi.

Babban sufeton makamai na MDD, Hans Blix, ya ce yana da muhimmanci a kaucewa sabanin ra'ayi da zarar an koma ga binciken makaman, yana mai fadin cewa yana son a ba su ikon binciken duk inda suke so a cikin kasar Iraqi.

A halin da ake ciki dai, Kwamitin Sulhun MDD yana nazarin wani daftarin kuduri sabo mai tsanani da Amurka ta gabatar, wanda ya gindaya sabbin sharrudan gudanar da bincike masu tsauri, tare da yin barazanar daukar matakan soja a kan Iraqi idan har ta ki bada hadin kai.

Bagadaza ta ce ba zata yarda da duk wani matakin kara tsaurin sharrudan gudanar da bincike ba.

XS
SM
MD
LG