Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Shiga Tsakani Na Afirka Ta Yamma Zasu Gana Da 'Yan Tawayen Ivory Coast Yau Alhamis - 2002-10-03


Masu shiga tsakani na Afirka ta Yamma sun ce suna shirin ganawa da sojoji masu tawaye yau alhamis domin tattauna shirin tsagaita bude wuta da nufin kawo karshen boren makonni biyu da yayi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Masu shiga tsakani daga Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, sun ce zasu tafi birni na biyu wajen girma a kasar. Bouake, cikin wani jirgin sama mai wsaukar ungulu na sojojin Faransa, domin tattaunawa da shugabannin 'yan tawaye tare ad sanin bukatunsu. Shugaban tawagar masu shiga tsakanin, Mohammed Chambas na kasar Ghana, ya shaidawa Muryar Amurka cewar yana sa ran za a shafe sa'o'i da yawa ana tattaunawa.

Masu shiga tsakanin suna fatan shirya ganawa tsakanin 'yan tawayen da gwamnati. Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ambaci firayim ministan Ivory Coast, Affi N'Guessan yana fadin cewa a shirye gwamnatinsa take ta tattauna da 'yan tawaye kan bukatunsu.

Wannan yunkurin sulhu yana zuwa a daidai lokacin da 'yan tawaye suka fadada yankunan dake hannunsu a arewaci da kuma tsakiyar kasar. A bayan Bouake, 'yan tawayen sun kama garuruwa da yawa cikin 'yan kwanakin nan a arewacin kasar, inda Musulmi suka fi yawa.

XS
SM
MD
LG