Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Biyu Cikin Kwanaki Biyar - 2002-10-08


Pakistan ta sake gwajin wani makami mai linzami, a karo na biyu a cikin kwanaki biyar.

Wata sanarwar da ma'aikatar tsaron Pakistan ta bayar, ta ce gwajin na yau an yi shi ne domin tabbatar da gaskiyar wasu bayanan da aka samu a gwajin ranar Jumma'a.

Tun da fari, kafofin labaran kasar sun ambaci majiyoyin gwamnati suna fadin cewa wannan makami mai linzami da ake harbawa daga doron kasa zuwa wani wuri a doron kasar, yana cin tazarar kilomita 800, kuma zai iya daukar kundojin nukiliya ko kuma na nakiya zalla.

A makon jiya, Pakistan da Indiya sun gudanar da gwajin makamai masu linzami sa'o'i kadan a tsakanin junansu.

Amurka ta bayyana bacin ranta, tana mai fadin cewa babu abinda gwaje-gwajen suka haddasa im ban da kara zaman tankiya a yankin da tuni ake fama da zaman dar-dar.

XS
SM
MD
LG