Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindiga Ya Addabi Mazauna Birnin Washington Da Kewaye - 2002-10-10


'Yan sandan yanki da na tarayya a nan Amurka suna binciken bindige wani mutum da aka yi har lahira cikin dare a wani gidan mai dake bayangarin birnin Washington.

Wakilin Muryar Amurka Victor Beatie ya ce harbewa da kashe wannan mutum da aka yi yayin da yake zuba mai cikin motarsa, yayi kama sosai da kashe-kashen da wani dan kwanton-bauna ya fara yi tun ranar 2 ga wannan wata na Oktoba.

Ana fargabar cewa wannan harbi da aka yi a garin Mannasas a Jihar Virginia, mai tazarar kilomita 50 daga nan Washington, aikin mutumin nan ne da ya kashe mutane shida, ya raunata wasu guda biyu cikin mako gudan da yayi yana bindige mutane haka siddan. Harbe-harben da aka yi duk sun ta'allaka ne a nan cikin birnin Washington da kuam jihohin Maryland da Virginia dake makwabtaka da ita.

Babban baturen 'yan sanda na yankin karamar hukumar Prince William, inda wannan harbi na baya-bayan ya wakana, Charlie Deane, ya ce duk da kamshi kamshin da ake ji, yana da wuya a yanzu a ce wannan aikin dan bindigar ne.

Ya ce suna hada kai tare da tuntubar sauran hukumomin dake binciken wadancan harbe-harbe, kuma zasu hada karfi wuri guda.

Biyu daga cikin mutanen da aka kashe a Jihar Maryland, an harbe su ne a gidajen mai.

Wani shaida a Jihar Maryland, ya shaidawa 'yan sanda cewa ya ga wasu mutane biyu cikin wata farar mota ko ta daukar kaya, ko kuma mai kama da karamar motar safa, suna tserewa daga wani wurin da aka yi harbi a wani gidan waya. 'Yan sanda a jihar Virginia ma, sun ce suna farautar wata farar mota mai kama da ta safa wadda aka gani tana tserewa daga wurin da aka yi wannan harbin. Har ila yau sun ce sun yi ma wani shaida tambayoyi game da harbin.

Tun lokacin da aka fara wadannan harbe-harbe dai, a kan harbi mutanen ne sau daya tak daga nesa da babbar bindigar kai farmaki ko kuma ta farauta. Babu wata alamar cewa mutanen da aka kashe din sun san juna. Kuma dukkan harsasan da ake samu, suna nuna cewar daga bindiga kwaya daya tak suka fito.

Kafofin yada labarai a nan birnin Washington sun ce a kusa da inda aka bindige aka raunata wani yaro mai shekaru 13 a kofar makarantarsu, 'yan sanda sun samu wani kati irin na masu duba, inda a jiki shi wannan makashi ya rubuta cewar, (wa iyazu billahi) "zuwa ga dan sanda, nine Allah."

XS
SM
MD
LG