Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Bai Wa Kamaru Tsibirin Bakassi - 2002-10-10


Kotun duniya ta yanke hukumcin cewa yankin nan na Bakassi mai arzikin man fetur da aka jima ana yin rikici a kai, na kasar Kamaru ne.

A cikin wannan hukumci da ta yanke a yau alhamis, kotun ta amince da hujjojin da kasar Kamaru ta gabatar cewa wannan yanki na Bakassi nata ne a karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin hukumomin mulkin mallaka na Jamus da na Ingila a farko-farkon karni na 20.

Wannan hukumci, tamkar shan kashi ne ga Nijeriya, wadda ta yi shekara da shekaru tana fada da Kamaru kan mallakin wannan tsibiri. Babban abinda ya sa kasashen biyu ke fada kan wannan yanki kuwa, shine dimbin man fetur din da aka yi imanin cewa yana kwance karkashin kasa a yankin, da kuma wuraren kamun kifi masu albarka.

Dukkan kasashen biyu suna da sojoji a wannan yanki na fadama dake mashigin ruwan Guinea. A yau alhamis aka sanya sojojin Nijeriya dake yankin cikin shirin ko-ta-kwana.

Dukkan kasashen biyu sun yi alkawarin mutunta hukumcin kotun. Babu damar daukaka kara game da wannan hukumci.

XS
SM
MD
LG