Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane Suna Mutuwa Daga Cututtukan Da Ake Iya Rigakafinsu - 2002-11-20


Hukumomi na kasa da kasa sun ce miliyoyin mutane suna mutuwa daga cututtukan da a kan iya kare kamuwa da su a saboda ba su da hanyar samun allurar rigakafi.

A cikin wani rahoton hadin guiwa da suka bayar yau laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da kuma Bankin Duniya, sun ce magungunan rigakafi ba su kaiwa ga mutanen da suka fi bukatarsu. Musamman wannan rahoton ya ambaci kasashen dake kudu da hamadar Sahara a Afirka, da kuma wuraren da aka fi fama da talauci da wadanda ke cikin lunguna a kasashe masu tasowa.

Rahoton ya ce allurar rigakafi tana ceton rayukan mutane miliyan 3 a kowace shekara, yayin da za a iya ceto rayukan wasu mutanen miliyan 3 idan da sun samu allurar rigakafi. Rahoton ya ce rabin yaran dake kasashen kudancin hamadar Sahara a Afirka ne kawai suke iya samun allurar rigakafin.

Rahoton yayi kiran da a kara sarrafawa tare da samar da kudin gudanar da ayyukan allurar rigakafi a kasashe masu tasowa. Ya ce samun karin dala miliyan 250 a shekara zai iya samar da allurar rigakafi ga karin yara miliyan 10.

XS
SM
MD
LG