Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kungiyar Musulmi Ta Ce Ba Ta Yarda Da Fatawar Kisan Da Aka Yi kan Marubuciya Ba - 2002-11-28


Babbar kungiyar Musulmin Nijeriya ta yi kira ga Musulmin kasar da su yi watsi da hukumcin kisan da wata jiha ta ce ta yanke kan wata marubuciyar da ta yi batunci ga addinin Musulunci.

A yau alhamis kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta bada sanarwa tana mai fadin cewa jami'an gwamnatin Jihar Zamfara ba su da ikon gabatar da Fatawa.

A ranar talata mataimakin gwamnan Jihar Zamfara ya yanke hukumcin a kan Isioma Daniel, yana mai kira ga dukkan Musulmin da su kashe ta. Ita ce ta rubuta wani sharhi cikin jaridar "This Day" inda take fadin cewa Annabi Muhammad (saw) zai iya zaben daya daga cikin masu takarar sarauniyar kyau ta duniya ta zamo matarsa. Wannan labarin ya haddasa mummunan fada a tsakanin Musulmi da Kiristoci a Jihar Kaduna, inda aka kashe mutane fiye da 200.

Isioma Daniel ta gudu daga Nijeriya, yayin da gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo ta ce ba zata kyale a zartas da wannan hukumci ba.

XS
SM
MD
LG