Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Britaniya Sun Bayyana Tababar Gaskiyar Dake Kunshe Cikin Rahoton Makamai Da Iraqi Ta Bayar - 2002-12-18


A gobe alhamis Amurka zata mayar da martani ga rahoton makaman da kasar Iraqi ta mikawa Majalisar Dinkin Duniya, MDD, kwanakin baya.

Sakataren harkokin waje, Colin Powell, da jakadan Amurka a MDD, John Negroponte, zasu yi sharhi kan rahoton makaman na Iraqi, a bayan babban sufeton makamai na MDD Hans Blix ya gabatar da jawabi gobe alhamisar ga Kwamitin Sulhun MDD. Wannan lamari yana zuwa a daidai lokacin da ita Amurka da kuma Britaniya suke bayyana tababar gaskiyar dake kunshe cikin rahoton makaman na Iraqi.

Sakataren harkoki wajen Britaniya, Jack Straw, ya ce ikiratin da Iraqi tayi cewar ba ta da makaman kare-dangi, a cewarsa, ba gaskiya ba ne. Firayim minista Tony Blair ya ce a bayan hutun Kirsimeti kasarsa zata bayyana sakamakon nazarin da ta yi wa rahoton makaman da Iraqi ta bayar.

Tun da fari dai, babban sufeton nukiliya na MDD, ya ce har yanzu ba su ga wata shaidar dake nuna cewa Iraqi ta koma ga kokarin kera makaman nukiliya ba tun bayan ayyukan bincike na karshe da aka gudanar a shekarar 1998.

Mohammed el-Baradei ya ce babu wata shaidar dake nuna cewa wani abu ya canja a cikin masana'antun nukiliya na Iraqi tun binciken karshe da aka yi shekaru hudun da suka shige.

XS
SM
MD
LG