Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Nausa Kudu Suka Kama Wani Garin Daga Hannun Sojojin Gwamnati - 2002-12-20


Wata kungiyar 'yan tawaye a yammacin Ivory Coast ta kara nausawa kudu, inda ta kwato wani garin daga hannun dakarun gwamnati, kwana biyu bayan da ta kwace garin Man.

A yau Jumma'a kungiyar mai suna "MPIGO" ta kwace garin Bangolo, mai tazarar kilomita 40 a kudu da garin Man.

Sojojin Faransa suna kilomita 40 a kudu da nan, kusa da garin Duekoue. Sun fada a yau Jumma'a cewar aikinsu shine na kare Faransawa dake zaune a Ivory Coast, sun kuma ce zasu yaki 'yan tawayen na kungiyar MPIGO idan suka yi kokarin tsallake kogin Sassandra dake kusa da nan.

'yan tawayen na kungiyar MPIGO sun bullo a karshen watan da ya shige na Nuwamba, kuma tun lokacin suke yakar gwamnati domin neman mallakin yammacin Ivory Coast. Ba a san ko suna da alaka da babbar kungiyar 'yan tawayen Ivory Coast dake rike da yankunan arewacin kasar ba.

'Yan tawayen arewacin masu suna "Kungiyar Al'ummar Ivory Coast", MPCI, ta fara tawaye a ranar 19 ga watan Satumba. Kungiyar ta bukaci shugaba Laurent Gbagbo da yayi murabus, a rubuta sabon tsarin mulki sannan a gudanar ad sabon zabe.

XS
SM
MD
LG