Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Kenya Suna Shirin Kada Kuri'a A Babban Zabe Mai Muhimmanci Gobe Jumma'a - 2002-12-26


Ana yakin zabe a rana ta karshe a kasar Kenya kafin babban zabe mai muhimmancin da za a gudanar gobe Jumma'a.

Ana kyautata zaton cewa dan takara na jam'iyyar hamayya, Mwai Kibaki, shine zai lashe zaben shugaban kasa, abinda zai kawo karshen mulkin shugaba Daniel Arap Moi. Tsarin mulki ya haramtawa Mr. Moi sake tsayawa, a bayan da ya shafe shekaru 24 yana mulkin kasar.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar KANU mai mulkin kasar, Uhuru Kenyatta, yana gwagwarmayar yarfar da yadda jama'a ke daukarsa a zaman dan amshin shatar da Mr. Moi ya tsayar domin ya kare muradun shugaban a bayan ya sauka daga kan mulki. Jam'iyyar KANU ce take mulkin Kenya tun lokacin da kasar ta samu 'yancinta a shekarar 1963.

Za a gudanar da wannan zabe a daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar talauci, rashin tsaro da kuma zarge-zargen zarmiya da cin hancin da ake yi wa gwamnati.

XS
SM
MD
LG