Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Tana Raba Sabuwar Allurar Rigakafin Sankarau A Afirka - 2003-02-07


Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce a yanzu tana raba wata sabuwar allurar rigakafi maras tsada wadda zata yaki wasu fitattun jinsunan kwayar cutar sankarau a kasashen bakar fata na Afirka, a saboda fargabar cewa a yanzu cutar tana bazuwa.

Cikin sanarwar da ta bayar alhamis, hukumar mai hedkwata a birnin Geneva ta ce wannan shiri nata ya kunshi tura allurai dubu 100 na wannan sabon maganin rigakafi zuwa Burkina Fasso domin yakar wani jinsin kwayar cutar sankarau da ake kira "W135" a turance. Wannan jinsi na kwayar cutar sankarau ya kama mutane dubu 1 da 300, ya kashe 244 a wannan kasa dake Afirka ta Yamma.

Za a sayar da kowace allura guda ta wannan sabon maganin rigakafin sankarau a kan dala daya da kwabo hamsin, watau kasa da sulusin kudin da aka saba biya kan kowace allura guda ta rigakafin sankarau. Kamfanin sarrafa magunguna na Britaniya mai suna Glaxo-Smith-Kline da kuma gidauniyar Bill Gates sune suka samar da kudin gudanar da wannan aikin.

XS
SM
MD
LG