Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Tayi Kashedin Cewa Zata Iya Kai Hari Kan Cibiyoyin Sojan Amurka - 2003-02-14


Wani babban jami'in jakadancin Koriya ta Arewa ya ce a yanzu, kasarsu tana da zarafin da zata iya kai hari kan cibiyoyin sojan Amurka a duk inda suke a fadin duniya idan har aka tsokane su.

Cikin hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Faransa, babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa a birnin Pyongyang, Ri Kwang Hyok, ya ce karfin da Koriya ta Arewa take da shi na iya kai hari ba ya da iyaka. Ya ce Koriya ta Arewa tana da makamai masu linzami dake cin dogon zango, kuma zata iya kai hari kan abokan gabanta dake nesa.

Darektan hukumar leken asirin Amurka ta CIA, George Tenet, ya ce watakila a yanzu haka Koriya ta Arewa tana da makami mai linzami dake iya daukar kundojin nukiliya,wanda kuma zai iya kaiwa ga yankunan dake gabayr yammacin Amurka.

A jiya alhamis, Japan ta ce a shirye take ta kai farmakin soja a kan Koriya ta Arewa idan har ta samu shaidar cewa kasar ta 'yan kwaminis tana shirin kai harin makamai masu linzami a kan ita Japan.

XS
SM
MD
LG