Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Kasashen Afirka Da Faransa A Paris - 2003-02-19


Shugaba Jacques Chirac na Faransa zai karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka 37 a taron kolin kwanaki ukun da za a yi a birnin Paris da nufin karfafa dangantaka tsakanin Faransa da Afirka.

A yau za a fara gudanar da taron koli na 22 na Kungiyar Kasashen Afirka Masu Magana da Harshen Faransanci, inda a yau din za a yi liyafar cin abincin dare a fadar Elysee. Taken taron na bana da za a kammala ranar Jumma'a, shine "Hada kai domin kulla sabon kawance tsakanin Afrika da Faransa."

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambaci majiyoyin gwamnati suna fadin cewa shugaba Chirac zai sake sabunta kudurin Faransa na taimakawa wajen habaka tattalin arziki da wanzar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.

Za a gudanar da wannan taron kolin yayin da ake yin gardama kan gayyatar da aka yi wa shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe kan ya halarci wannan taron, duk da haramcin da Kungiyar Tarayyar Turai tayi masa na shiga cikin wata kasarta. Faransa dai memba ce ta tarayyar turai.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Faransa da Zimbabwe sun soki gwamnatin Faransa a saboda gayyatar Mr. Mugabe da ta yi.

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ba zai halarci taron kolin ba, a maimakon haka zai tura sabon firayim ministan kasar, Seydou Diarra.

Shugaban na Ivory Coast ya fusata Faransa a bayan da ya tsame hannu daga yarjejeniyar zaman lafiyar da Faransa ta taimaka aka kulla a tsakaninsa da 'yan tawaye a watan janairu.

XS
SM
MD
LG