Babban jami'in MDD dake kula da harkokin samar da ruwan sha ya ce za a iya warware akasarin matsalolin karancin ruwa a duniya idan za iya kashe dala miliyan dubu 100 a kowace shekara.
Gordon Young na Hukumar samar da ruwa ta MDD ya shaidawa 'yan jarida a Tokyo cewa mutane miliyan biyu suke mutuwa kowace shekara a sanadin cuce-cuce amsu alaka da ruwa.
Ya ce za a iya warware kusan dukkan matsalolin dake tattare da ruwa idan za a kashe dala miliyan dubu 50 zuwa dubu 100 a kowace shekara. Amma Mr Young ya ce gardamar siyasa ce take hana kashe irin wannan kudi.