Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ce Zata Yi Mulkin Kasar Iraqi Kafin A Kafa Gwamnatin Riko - 2003-03-27


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce yana sa ran Majalisar Dinkin Duniya, MDD, zata taka rawar tsara gwamnatin da za a kafa a kasar Iraqi a bayan yaki.

A lokacin ad yake bayar ad shaida gaban 'yan majalisar dokoki jiya laraba, Mr. Powell ya bayyana shirin da Amurka ta yi na mulkin kasar Iraqi a bayan ta hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.

Mr. Powell ya ce a karkashin wannan shiri nasu, za a kafa gwamnatin mulkin soja da zarar an kare yaki, sannan kuma sai Amurka ta yi mulkin kasar a zaman farar hula. Amma kuma ya ce a daidai lokacin da Amurka take mulkin kasar ta Iraqi, za a yi kokarin kafa gwamnatin rikon kwarya ta Iraqi tare da taimakon MDD.

Mr. Powell ya ce gwamnatin rikon kwaryar da za a kafa, daga baya, zata kunshi 'yan Iraqi dake zaman gudun hijira da wadanda ke zaune a cikin kasar, kuma ita ce zata zamo tushe ko harsashin sabuwar gwamnatin farar hula da za a kafa a Iraqi.

A can MDD kuwa, babban sakatare Kofi Annan yayi kira ga Kwamitin Sulhu da ya dauki matakan gaggawa na samar da kayayyakin agaji da al'ummar Iraqi ke bukata.

A lokacin ad yake magana a wajen taron gaggawa na Kwamitin Sulhun, Mr. Annan ya bayyana takaicin cewa an kasa hana barkewar yaki.

Kungiyar Kasashen Larabawa da kuma ta Kasashen 'Yan Babu-Ruwanmu, sune suka bukaci da a yi wannan taron gaggawa da za a ci gaba da yinsa a yau alhamis.

XS
SM
MD
LG