Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Mai Sun Ce Suna Dari-Dari, Duk Da Yarjejeniyar Sulhun Da Aka Kulla A Nijeriya - 2003-03-27


Manyan kamfanonin mai na kasa da kasa sun ce ba zasu koma aikin tonon mai a yankin kudu maso gabashin Nijeriya ba, duk da cewa 'yan dabar kabilun yankin sun yarda zasu kawo karshen fadan da suka yi makonni suna gwabzawa.

Kamfanonin man sun fada a yau alhamis cewa zasu koma aikin tonon mai ne kawai a yankin Niger Delta idan har suka tabbatar da cewa babu wani abinda zai taba lafiyar ma'aikatansu.

Fadan kabilanci yayi sanadin mutuwar mutane akalla 60, ya kuma tilastawa kamfanonin mai guda uku rufe ayyukansu an tonon mai baki daya a Nijeriya. Wannan ya rage yawan man da kasar take hakowa a kowace rana da kashi 40 daga cikin 100.

A jiya laraba, a bayan da suka gana da jami'an gwamnatin Jihar Delta,'yan ta-kifen kabilar Ijaw sun ce zasu daina fada da sojojin gwamnati da kuma kishiyoyinsu 'yan kabilar Itsekiri. 'Yan kabilar at Ijaw sun ce suna son samun wakilcin siyasar da ya kamace su.

Har ila yau, shugabannin kabilar ta Ijaw sun bukaci diyya daga kamfanonin mai, wadanda suka ce suna gurbata musu ruwayen kamun kifi.

Wannan fada ya barke a lokacin da 'yan kabilar ta Ijaw suka gwabza da sojoji masu gadin cibiyoyin mai a yankin. Daga nan 'yan ta-kifen na Ijaw suka juya suka kai farmaki kan 'yan kabilar Itsekiri, wadanda suka ce suna neman kanainaye harkokin siyasa.

XS
SM
MD
LG