Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu zata yanke hukumci. - 2003-04-10


A yau alhamis ne, kotun tarayyar Nigeriya a Abuja zata yanke hukumcin kararrakin da wasu jam'iyyu suka kai suna bukatar a dage zaben kasar da za a fara daga jibi Asabar.

Jam'iyyun NDP da UNPP tare da goyon-bayan wasu kananan jam'iyyu su kimanin 14 ne suka gurfana a Mashari'anta suna kalubalantar hukumar zaben kasar game da gudanar da zaben.

Ita jam'iyyar NDP ta ce, hukumar ta karya sashin dokar zaben kasar, wanda ya tanaji a kammala tsarawa, da yin gyara da gabatar da koke-koke ga littafin masu zabe kwanaki 60 kafin a fara kowane irin zabe a kasar. Ita kuma jam'iyyar UNPP ta ce, har yau hukumar ta kasa raba katunan zabe na hakika, wanda shi ma sabawa wani sashi na dokar zaben ne.

To amma lauyoyin hukumar zaben sun ce hukumar ta kiyaye da dukkanin sassan dokar zaben, kuma ba su yi mata karen tsaye ba. Hukumar ta ce ta rigaya ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben cikin nasara, kuma ba za a ci karo da wata matsala ba.

A halin yanzu kuma masu zabe a wasu sassan kasar Nigeriya sun yi korafin cewa har yanzu ba su karbi katunan rijistarsu ba, kwanaki biyu kacal kafin a fara gudanar da babban zaben kasar.

Fiye da 'yan kasar ta Nigeriya miliyan 61 ne suka cancanci yin zaben wakilan majalisar dokokin kasar na ranar asabar da kuma na shugaban kasa da gwamnonin jihohin kasar a ranar 19 ga wannan Wata na Afirilu.

Masu fashin bakin al'amurra sun ce akasarin cibiyoyin da ya kamata su fara raba katunan zabe duk a rufe suke.

Wata hadakar kananan jam'iyyun adawa sun bukaci a dage zaben saboda rashin kyakkyawan shiri.

XS
SM
MD
LG