Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indonesiya Ta Kaddamar Da Farmakin Soja A Aceh... - 2003-05-19


Indonesiya ta kaddamar da farmakin soja a Aceh, a bayan da aka tashi baram-baram daga tattaunawar neman zaman lafiya da 'yan awaren lardin.

A yau litinin daruruwan sojan laima suka dira cikin Banda Aceh, babban birnin lardin, da kuma yankunan dake kusa da nan, yayin da jiragen saman kai farmaki samfurin O-V-10 kirar Amurka suka yi ta harba rokoki a sansanonin 'yan tawaye.

Shugabar Indonesiya, Megawati Sukarnoputri, ita ce ta bada umurnin kai farmakin na soja, a bayan da aka watse dutse hannun riga daga tattaunawar neman zaman lafiya a tsakanin gwamnatin Indonesiya da Kungiyar Kwatar 'Yancin Aceh jiya lahadi a birnin Tokyo.

Shugaba Megawati ta ayyana kafa dokar soja a lardin, tana mai cewa 'yan tawaye sun ki yarda da tayin gwamnati na ba su ikon cin gashin kai na musamman domin su ajiye makamansu.

Dokar sojar, wadda ta fara aiki da karfe 12 na daren jiya agogon kasar, watau karfe 6 na maraicen jiya lahadi agogon Nijeriya, zata yi aiki na watanni shida, kuma ana iya kara wa'adinta. Dokar ta bai wa jami'an tsaro karin ikon kafa dokar hana yawo, da bincike tare da hana mutane shiga ko fita daga cikin yankin.

Har ila ya, 'yan sanda suna sake tsare wasu manyan jami'an shawarwari na 'yan tawaye su biyar, wadanda aka sako raar sabar kafin a fara tattaunawa.

Wani madugun 'yan tawaye, Malik Mahmud, ya ce a shirye dakarunsu suke su gwabza da na gwamnatin Indonesiya.

An kashe mutane fiye da dubu 10, akasarinsu fararen hula, a cikin shekara da shekarun da aka yi ana gwabza fada a lardin na Aceh.

XS
SM
MD
LG