Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Shari'ar Turawan Da Ake Zargi Da Kulla Makrkashiyar Hambarar Da Gwamnatin Afirka Ta Kudu - 2003-05-19


Wani alkali a Afirka ta Kudu ya dage shari'ar wasu turawa 232 da ake zargi da kulla makarkashiyar hambarar da gwamnatin kasar har sai makon gobe.

Alkalin ya dage wannan shari'a har sai ranar 26 ga watan Mayu a bayan da mutanen da ake tuhumar suka ce suna son daukar lauyoyinsu maimakon na gwamnati da aka ba su.

Masu gabatar da kara suna zargin cewa mutanen 'ya'yan wata kungiyar fifita jinsin turawa ce da ake kira Boeremag. An yi zargin cewa kungiyar tana neman ganin kafa kasar turawa zalla ta hanyar kora ko kashe bakaken fata da Asiyawa da duk mutanen dake kalubalantar akidarsu ta kasar turawa jinsin Afrikaner zalla.

An yi zargin cewa kungiyar ce ta kai hare-haren bam bara a fadin kasar, inda har mutum guda ya rasa ransa.

XS
SM
MD
LG