Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Gabatar Da Kuduri Kan Kafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Kwango-Kinshasa - 2003-05-28


Faransa ta gabatarwa da Kwamitin Sulhun MDD daftarin kuduri na kafa rundunar kiyaye zaman lafiyar gaggawa da za a girka a yankin Ituri na gabashin Kwango-Kinshasa.

Ana kyautata zaton Kwamitin Sulhun zai jefa kuri'a kan wannan kuduri nan da karshen mako. Kwamitin sulhun yana taro yau laraba cikin sirri a kan batun kasar ta Kwango.

An tsara wannan kudurin ne domin karfafa sojojin MDD su 700 dake Ituri a yanzu haka, amma kuma ba su da iko, ko kayan da suke bukata domin kashe wutar kazamin fadan da ake gwabzawa a tsakanin sojojin sa kai na kabilun yankin dake neman ikon mallakar albarkatun kasar dake can.

Faransa da Britaniya da Tarayyar Turai, da Pakistan da Nijeriya da kuma Afirka ta Kudu duk sun ce zasu bada gudumawa ga wannan runduna.

Tun da fari a yau laraba, rundunar ta MDD dake Ituri ta bada rahoton cewa yawan mutanen da suka mutu a fadan da ake yi a can ya karu zuwa 380, da yawa daga cikinsu fararen hula.

Har ila yau rundunar ta zargi 'yan kabilar Hema da laifin watsa akidojin gaba ta rediyo domin kuntatawa fararen hular da suka nemi mafaka a zauren MDD dake garin.

XS
SM
MD
LG