Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Na Shirin Gudanar Da Sabon Aiki A Kasar Somaliya - 2003-05-28


Bankin Duniya yana shirin gudanar da sabon aiki a kasar Somaliya, aikinsa na farko a kasar tun shekarar 1991.

Bankin ya ce wannan shiri na Somaliya na hadin guiwa ne da Hukumar Raya Kasashe ta MDD.

Babu gwamnatin tarayya a kasar Somaliya, kuma kungiyoyin sojan sa kai na kabilu dabam dabam ne suke gudanar da harkokin yankunan kasar.

Wannan sabon aikin zai hada da tattara bayanai domin auna tattalin arzikin kasar, da kafa wani tsarin sayar da dabbobin da ake kiwo a kasar a waje tare da tallafawa kokarin dakile yaduwar cutar kanjamau ta AIDS ko SIDA a kasar.

Ana sa ran kashe dala miliyan uku da rabi domin gudanar da wannan aiki na Somaliya.

XS
SM
MD
LG