Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawar Zimbabwe Yana Fuskantar Sabon Laifin Cin Amanar Kasa - 2003-06-09


Madugun adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya bayyana a gaban kotu inda aka tuhume shi da wasu sabbin laifuffuka na cin amanar kasa, yayin da hukumomi suka titsiye wani madugun adawar na biyu domin yi masa tambayoyi a game da zanga-zangar makon jiya.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bada labarin cewa wata kotu a birnin harare ta ki yarda ta bayar da belin Mr. Tsvangirai, wanda ke shugabancin jam'iyyar adawa ta M.D.C.(Movement for Democratic Change).

A ranar Jumma'a aka damke Mr. Tsvangirai bisa zargin cewa ya zuga magoya bayansa su hambarar da gwamnatin kasar a lokacin zanga-zangar da aka yi a makon jiya.

Har ila yau, 'yan sanda sun yi wa babban sakataren 'yan adawa, Welshman Ncube, tambayoyi game ad zanga-zangar.

An shirya zanga-zangar ta mako guda da nufin tilastawa shugaba Robert Mugabe tattaunawa da 'yan adawa kan matsalolin siyasa da na tattalin arziki da kasar take fuskanta.

XS
SM
MD
LG