Jami'an shiga tsakani na Afirka ta Yamma suna fatar yin tattaki zuwa Liberiya a yau talata domin suyi kokarin kulla shirin tsagaita wuta a tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen dake neman shugaba Charles Taylor yayi murabus.
A jiya litinin, jami'an kungiyar ECOWAS, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar neman zaman lafiyar da ake yi a Ghana, sun tashi domin yin tattakin da zai hada da kasashen Guinea da Saliyo.
A yau talata suke shirin tattaunawa da shugaba Charles Taylor a Monrovia, babban birnin kasar.
Tun da fari, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi kiran da a kawo karshen fadan da ake yi nan take a Liberiya. Wannan kira na MDD ya zo 'yan sa'o'i kadan a bayan da sojojin Faransa suka yi amfani da jiragen helkwaftoci masu saukar ungulu domin kwashe 'yan kasashen waje su fiye da 500, a yayin da sojojin 'yan tawaye suka doshi Monrovia.
A ranar lahadi, babbar kungiyar 'yan tawaye ta Liberiya, L.U.R.D., ta bai wa shugaba Taylor wa'adin kwanaki uku da ya sauka ko kuma zasu kai farmakin kwace babban birnin kasar.