Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tura Sojoji Zuwa Liberiya Da Mauritaniya - 2003-06-10


Amurka ta tura sojoji sittin da tara, da wasu jiragen saman da ba a bayyana yawansu ba, domin karfafa tsaron ofisoshin jakadancinta a Liberiya da Mauritaniya, tare da shirye-shiryen kwashe Amurkawa daga wadannan kasashe idan bukatar hakan ta taso.

Shugaba Bush ya fadawa majalisar dokoki jiya litinin a cikin wata wasika cewar sojoji 35 sun isa Liberiya, inda sojojin 'yan tawaye masu adawa da shugaba Charles Taylor suka isa unguwannin dake dab da ofishin jakadancin Amurka.

Ya ce nan gaba a yau talata sojoji 34 zasu isa Nouakchott, babban birnin Mauritaniya, inda sojojin gwamnati ke kokarin kashe wutar wani yunkurin juyin mulki.

Har ila yau an tura aka ajiye wasu jirage da ma'aikatansu a Dakar Senegal, domin rage tsawon lokacin da zai dauka idan har bukatar kwashe Amurkawa daga wadannan kasashe biyu ta taso.

Mr. Bush ya ce koda yake wadannan sojoji sun yi shirin fada, manufar tura su ita ce kare Amurkawa da dukiyarsu a wadannan kasashe. Ma'aikatar harkokin waje ta umurci ma'aikatan ofishin jakadancin da ayyukansu ba su da matukar muhimmanci da su bar Liberiya, ta kuma shawarci Amurkawan dake kasar da su ma su fice.

XS
SM
MD
LG